Kila Chelsea da Arsenal su kara

Chelsea da Arsenal
Image caption Misali Idan Chelsea ta yi canjaras 0-0 Arsenal ta ci 2-1 za a yi wasan raba gardama tsakaninsu

Mai yuwuwa Chelsea da Arsenal su yi wasan raba gardama na neman matsayi na uku a Premier domin zuwa Gasar Zakarun Turai.

Hakan na iya tabbata ne idan kungiyoyin suka kammala wasanninsu na karshe da maki iri daya.

Duk wadda ta yi nasara a wasan ita zata zama ta uku a tebur din Premier wadda ke da damar zuwa Gasar Zakarun Turai.

Chelsea wadda take matsayi na uku a gaban Arsenal da maki biyu za ta karbi bakuncin Everton ranar Lahadi.

Yayin da Arsenal kuma za ta bakunci Newcastle a ranar.

Kungiyoyin zasu kasance da maki dai-dai-wa-dai-da idan Chelsea ta tashi canjaras da ci ko ba ci.

Ita kuma Arsenal ta yi galaba da ci biyu ko fiye da haka amma da bambancin kwallo daya tsakaninta da Newcastle din.

Kungiyoyi uku na farko a Premier zasu shiga Gasar Zakarun Turai mai zuwa kai tsaye a matakin rukuni rukuni.

Kungiyar da ta zama ta hudu kuwa za ta shiga zagaye na uku na neman shiga Gasar ne (play-off).

Idan har wasan ya tabbata to za a yi shi ne a wani filin wasa na 'yan-ba-ruwanmu a wata rana da za a tsaida.