Lampard ya sabunta kwantiragi a Chelsea

Frank Lampard
Image caption Shirin dawowar Mourinho ake ganin ya sa Lampard tsayawa a kungiyar

Frank Lamprad ya kulla kwantiragin shekara daya da Chelsea bayan da kungiyar ta dauki Kofin Europa.

Kwantiragin dan wasan na tsakiya na yanzu zai kare ne a watan Yuni kuma ana ta tantama game da ci gaba da zamansa a kungiyar.

Ya ce , ''na yi matukar farin ciki, kowa ya san ina son ci gaba da zama.''

''Na godewa Mr Abramovich da ya tabbatar min da wannan fata.

Ina kaunar wannan klub da ma'aikata da 'yan wasan musamman ma magoya bayansa.''

Lampard mai shekaru 34 ya zama dan wasan da ya fi ci wa kungiyar kwallaye a tarihi.

Bayan da ya wuce Bobby Tambling wanda ya ke da tarihin cin kwallaye 202 a makon da ya wuce.

Lampard ya bugawa Chelsea wasanni 607 tun lokacin da kungiyar ta sayo shi daga West Ham a watan Yuni na 2001.

Ana ganin tsohon kociyan kungiyar Jose Mourinho ne zai sake dawowa ya maye gurbin Rafeal Benitez mai rikon kwarya.

Kuma ana danganta tsayawar Lampard din da shirin dawowar Mourinho.