FA ta Ingila ta yi dokar wariya

Suarez da Evra
Image caption Suarez ya ci mutuncin Evra ta wariyar launin fata

Duk dan wasan da aka samu da laifin cin mutunci na wariyar launin fata za a hana shi akalla wasanni 5 kamar yadda Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA ta zartar.

Hukuncin zai kuma shafi masu laifin nuna bambancin addini ki jinsi ko kuma nakasa.

Kuma dan wasan da ya sake aikata laifin za a hana shi wasanni goma da kuma tarar kudi.

A taron Hukumar FA din da aka yi ranar Alhamis aka amince da wannan doka wadda za a fara amfani da ita daga kakar wasanni ta gaba.

A watan da ya gabata Hukumar kwallon kafa ta Turai ta bullo da hukuncin hana dan wasa ko jami'in wasa wasanni goma a kan laifin wariyar launin fata.