Maria Sharapova ta samu koma-baya

Maria Sharapova
Image caption Maria Sharapova ta janye daga gasar Italian Open

An samu koma-baya a shirye-shiryen Maria Sharapova na halartar gasar French Open bayan da ta janye daga gasar Italian Open saboda rashin lafiya.

'Yar wasan tennis din 'yar kasar Rasha, wacce za ta kare kambunta a gasar ta French Open daga ranar 26 ga watan Mayu, na shirin karawa ne da Sara Errani a wasan kusa da na kusa da na karshe, wato quarter final, a gasar ta Italian Open ranar Juma'a.

Sharapova ta rubuta a shafinta na Twitter cewa: "A yi hakuri, ban kammala warwarewa ba daga cutar da ta kwantar da ni makon jiya, kuma ta sake dawowa".

Tuni dai Serena Williams ta shiga zagayen kusa da na karshe bayan nasarar da ta yi a kan 'yar Spain, Carla Suarez Navarro.

Wannan nasara ita ce ta 22 a jere da Williams ta yi; hakan kuma na nufin ta zarta kokarinta na baya, inda ta yi nasara sau 21 a jere a shekarun 2002 da 2003.

Karin bayani