Nadal ya lallasa Federer ya dauki kofi

Rafeal Nadal
Image caption Federer ya ce Nadal bai yi kurakurai ba da yawa kuma ya ji dadin wasan sosai

Rafeal Nadala ya lallasa Roger Federer cikin mintuna 68 kacal ya dauki kofinsa na Gasar Italiyan Open na Bakwai.

A karawa talatin da suka yi a tarihi zakarun tennis din biyu da kowannensu ya dauki manyan kofuna 28, Nadal dan Spaniya ya yi galaba da maki 6-1 6-3.

Nadal wanda kafin yanzu ya dauki kofin Gasar sau shida kuma ya zo na biyu sau biyu a karo takwas da aka yi Gasar.

Zai zama gwani na hudu na tennis a duniya sakamakon wannan nasara.