An kammala Gasar Premier

Wasan Ferguson na karshe da West Brom
Image caption Ferguson ya kasa samun nasara a wasansa na 1,500 na karshe da West Brom

A ranar Lahadin nan aka kammala gasar kwallon kafa ta Premier ta Ingila inda dukkanin kungiyoyi 20 suka yi wasanninsu na karshe na 38.

Manchester United wadda ta bi West Brom gida ta yi canjaras da su 5-5 inda ta kammala gasar da maki 89.

Manchester City a gidanta ta sha kashi a hannun Norwhich da ci 3-2 ta gama gasar ta bana a matsayi na biyu da maki 78.

Chelsea ta samu damar zuwa Gasar Zakarun Turai bayan ta sami matsayi na uku da ta ci Everton 2-1 a Stamford Bridge, inda ta samu maki 75.

Arsenal ita ma ta samu damar shiga Gasar ZakarunTuran bayan da ta je gidan Newcastle ta yi mata daya mai ban haushi, ta zama ta 4 da maki 73.

Duk da nasarar da Tottenham ta samu a kan Sunderland da ci 1-0 ba ta samu cancantar shiga Gasar Zakarun Turai ba saboda ta kammala a matsayi na biyar da maki 72.

Sakamakon Wasannin

Chelsea 2 - 1 Everton ; Liverpool 1 - 0 QPR

Man City 2 - 3 Norwich; Newcastle 0 - 1 Arsenal

Southampton 1 - 1 Stoke ; Swansea 0 - 3 Fulham

Tottenham 1 - 0 Sunderland ; West Brom 5 - 5 Man Utd

West Ham 4 - 2 Reading ; Wigan 2 - 2 Aston Villa