West Ham na son sayen Carroll

Andy Carroll
Image caption Andy Carroll ya ciwa Ingila kwallaye 2 a wasanni 9

Liverpool ta amince ta saida wa West Ham Andy Carroll a kan fam miliyan 15 sai dai dan wasan mai shekaru 24 bai yanke shawara ko zai koma kungiyar dun-dun-dun ba.

Sakamakon zuwan Brendan Rodgers Liverpool da kuma sabon tsarin wasan kungiyar kwallaye 6 kawai Carrol ya ci wa Liverpool a wasanni 44 a don haka aka bada aron sa ga West Ham a watan Agusta na 2012.

Duk da ciwon guiwa da ya yi fama da shi a watan Disamba kokarin da ya yi na cin kwallaye 7 a kakar wasannin ya sa kociyan ya ke son ya zauna dun-dun-dun a West Ham.

A halin da ake ciki kuma Carroll ya janye daga cikin tawagar 'yan wasan Ingila da za ta yi wasannin sada zumunta da Jamhuriyar Ireland da kuma Brazil saboda raunin da ya ji a dunduniya.