Liverpool za ta dauki Kolo Toure

Kolo Toure
Image caption Kolo Toure zai zama dan wasa na farko mai shekaru sama da 24 da Brendan Rodgers wanda ba ya son manya zai yi

Liverpool za ta nemi Kolo Toure da zarar kwantiraginsa da Manchester City ta kare a watan Yuni.

Saboda Jamie Carragher yayi murabus Liverpool na neman 'yan baya guda biyu kuma dan wasan Schalke Kyriakos Papadopoulos ne kan gaba.

Toure yanzu yana tare da tawagar City a Amurka a rangadin wasanninta na bayan kaka kuma ana sa ran da sun dawo za a ci gaba da maganar komawarsa Liverpool din.

Kolo Toure mai shekaru 32 wanda ya koma Man City daga Arsenal a watan Yuli na 2009 a kan fam miliyan 14 sau 18 kawai ya bugawa City a kakar da ta kare.

Tun lokacin da aka dakatar da shi tsawon watanni 6 a kakar 2010-11saboda samunsa da laifin amfani da kwayar da aka haramta tun sannan bai dawo kan ganiyarsa ba.