Fulham ta dauki Boateng da Amorebieta

Derek Boateng
Image caption Derek Boateng ya ce ya rattaba hannu a kan kwantiragin shekara biyu da Fulham

Dan wasan tsakiya na kasar Ghana, Derek Boateng, ya bayar da sanarwa cewa ya kammala shirin komawa Gasar Premier ta Ingila inda zai buga wa Fulham daga kungiyar Dnipro ta Ukraine.

Dan wasan mai shekaru 30 da haihuwa ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa: "Na rattaba hannu a kan kwantiragin shekara guda da kungiyar kwallon kafa ta Fulham! Ina farin ciki da ganin wannan yarjejeniya ta tabbata!

"Ina godiya ga Allah, da iyali na, da duk masu goyon baya na!"

Boateng ya kuma wallafa hotonsa dauke da rigar Fulham a filin Motspur Park, inda kungiyar ke atisaye.

Har yanzu dai Fulham ba ta tabbatar da kulla yarjejeniyar a hukumance ba, amma ga alama dan wasan, wanda ya taba buga wa Getafe, da Cologne, da Beitar Jerusalem, shi ne mutum na biyu da kungiyar ta saya bayan dan wasan baya Sascha Riether ya amince da kwantiragin dindindin sakamakon hazakar da ya nuna yana dan wasa na aro.

Kocin kungiyar ta Fulham, Martin Jol, ya jima yana so ya sayi Boateng amma takaddama tsakanin dan wasan da kungiyarsa [Dnipro] ta hana.

Haka kuma kungiyar ta Fulham ta dauki dan wasan baya Fernando Amorebieta dan kasar Venezuela.

Dan wasan mai shekaru 28 ya kulla yarjejeniya ta shekaru 4 da Fulham bayan shekaru 8 a kungiyar Athletic Bilbao.

Kawo yanzu Fulham ta dauki 'yan wasa 3 ke nan na kakar wasa ta gaba, idan aka hada da Sascha Riether wanda ya ke zaman aro a kungiyar daga Cologne.

Karin bayani