Kofin Zakarun Turai: Gotze ya ji rauni

Mario Gotze
Image caption Sau 22 Mario Gotze yana buga wa Jamus wasa inda ya ci kwallaye 5

Gwanin dan wasan Borussia Dortmund Mario Gotze ba zai buga wasan karshe na kofin Zakarun Turai da za su yi da Bayern Munich wadda zai koma ba saboda rauni.

Gotze mai shekaru 20 bai buga wani wasa ba tun watan da ya wuce lokacin da ya ji rauni a cinyarsa a wasansu da Real Madrid na kusa da karshe karo na biyu.

A watan Afrilu aka sanar cewa Gotze zai koma Bayern a kakar wasanni ta gaba a kan fam miliyan 31 da rabi.

Cinikin nasa ya sa ya zama dan wasan Jamus mafi tsada a tarihi idan ya koma Bayern Munich din a ranar 1 ga watan Yuli.

Tsohon dan wasan Jamus Franz Beckenbauer ya bayyana Gotze da cewa iri daya ya ke da Lionel Messi Gwarzon dan wasan Duniya na shekara karo hudu.