Kamaru ta nada Finke a matsayin koci

Volker Finke
Image caption Kamaru ta nada Volker Finke a matsayin sabon kocin Indomitable Lions

Kamaru ta bayyana Bajamushe Volker Finke a matsayin sabon kocin tawagar kwallon kafa ta kasar, wato Indomitable Lions. Shi ne zai maye gurbin Jean-Paul Akono.

A da dai rahotanni sun nuna cewa Akono da mataimakansa ne za su jagoranci tawagar a wasannin da ta buga da Togo ranar 9 ga watan Yuni da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ranar 16 ga watan masu muhimmanci na neman gurbi a Gasar Kofin Duniya.

Sai dai kuma kasancewar Akono bai gama murmurewa ba daga lalurar da ake tunanin bugun zuciya ce da ta kama shi a karshen mako, mai yiwuwa Finke ya fara aiki kafin lokacin da aka zata.

An dai yi amanna cewa an so a baiwa tsohon kocin Faransa, Raymond Domenech da Antoine Kambouare mukamin.

Karin bayani