Mali za ta kai kocinta kara gaban FIFA

Patrice Carteron
Image caption Mali ta ce za ta kai Patrice Carteron gaban FIFA saboda ya saba ka'idojin kwantiraginsa

Hukumar Kwallon Kafa ta Mali ta ce za ta kai karar kocin tawagar 'yan wasanta, Patrice Carteron, a gaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, wato FIFA, saboda ya saba ka'idojin kwantiraginsa da komawarsa TP Mazembe.

Kocin dan asalin kasar Faransa ya rattaba hannu a kan kwantiragin shekaru biyu da kungiyar kwallon kafar ta TP Mazembe ta Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ne duk da cewa kwantiraginsa da tawagar ta The Eagles ba ta kare ba sai watan Yuli.

Carteron ya yi tayin ci gaba da jagorancin tawagar ta Mali har sai sun buga wasanni biyu na neman gurbi a Gasar Kofin Duniya.

Amma mataimakin shugaban Hukumar Kwallon Kafar Mali, Moussa Konate, ya ce, "Ba mu da zabi illa mu kai batun gaban FIFA".

'Yan wasan Malin dai sun yi kankankan a saman rukunin da suke na neman gurbin, kuma kasancewar suna da wasannin gida tsakaninsu da Rwanda da kuma Benin, daf suke da hawa wani matsayi da ka iya sama musu gurbi a Gasar Kofin Duniya a karo na farko.

Carteron, wanda shawararsa ta tafiya ta zo wa 'yan Malin da ba-zata bayan ya kai tawagarsu matsayi na hudu a Gasar Kofin Kasashen Afirka a watan Fabrairu, ya ce zai jagorance su su buga wasannin watan Yuni kafin ya tafi.

Ya shaida wa gidan rediyon Faransa cewa: "Ina ganin abin da ya dace ke nan saboda ni na zabo 'yan wasan".

Ya kuma kara da cewa da ma dai ko ta halin kaka ya yanke shawarar barin Mali a karshen wasannin neman gurbin saboda tangal-tangal din siyasar da kasar ke fama da shi.