"Akwai kalubalen kara yawan 'yan Ingila a Premier"

Sabon shugaban hukumar kwallon Ingila Greg Dyke ya ce daya daga ciki kalubalen da zai fuskanta shine na kara yawan matasa 'yan Ingila da ke taka leda a gasar Premier.

Sabon shugaban hukumar mai shekarun haihuwa zai karbi ragamar aikin ne da Shugaba mai barin gado David Bernstein a watan a ranar 13 ga watan Yuli.

Greg Dyke zai karbi aikin shugabancin hukumar ne a daidau lokacin da yawan matasa yan Ingila a gasar ta Premier na kara raguwa.

An kiyasta 'yan wasan Ingila da ke taka leda a gasar Premier a kashi 36 cikin dari a yayinda kuma a kasar Spain yawan kasar da ke taka leda a gasar Laliga sun kai kashi 61.

A faransa kuwa kashi sittin ne na 'yan kasar ke taka leda a gasar Ligue One a yayinda kuma a Jamus kashi 47 ne.

Sai kuma a kasar Italiya inda kashi 46 ne na kasar ke taka leda a gasar Serie A.