Martinez ya bar Wigan ya nufi Everton

Roberto Martinez
Image caption Martinez yayi kociyan Swansea kafin ya koma Wigan

Kociyan Wigan Roberto Martinez ya ajiye aikin horad da 'yan wasan Wigan kuma zai tattauna da Everton domin maye gurbin David Moyes.

Martinez mai shekaru 39 dan Spaniya ya jogaranci Wigan ta kafa tarihi inda ta dauki Kofin Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila FA a bana amma kuma ya kasa kare su daga faduwa daga Premier.

Shugaban Wigan Dave Whelan ya ce ''Everton ta tuntube ni ranar Juma'a domin samun izinin magana da kociyan wanda shi ma yake son tafiya kuma na amince.''

A watan Yuni na 2009 Martinez ya kama aiki da Wigan kuma a watan Yuni na 2011 Aston Villa ta nemi daukan sa amma yaki tafiya kazalika a bara ma an yi tsammanin zai koma Liverpool.

Tun bayan da ya fara aikin horad da 'yan wasan Wigan yayi kokarin tabbatar da klub din a Gasar Premier duk da rashin isassun kudade idan aka kwatanta shi da takwarorinsa.