Tafiyar Zaha asara ce gare mu: Palace

Wilfried Zaha
Bayanan hoto,

Idan za a sake bayar da Zaha aro a Premier zamu neme shi inji shugaban Crystal Palace

Shugaban Crystal Palace Steve Parish ya ce ba su da niyyar dawo da Wilfried Zaha kungiyar a matsayin aro daga Manchester United.

Zaha mai shekaru 20 ya kulla yarjejeniyar komawa Manchester United a watan Janairu amma kuma ya tsaya a Crystal Palace ya taimaka musu samun shiga Gasar Premier.

Dan wasan na Ingila ya ci wa Palace kwallaye biyu a gasar neman kungiyar da zata shiga Premier (play-off) a wasan kusa da karshe da Brighton.

Kuma ya samo musu bugun fanareti a wasan karshe da suka yi da Watford wanda Kevin Phillips ya ci, suka samu shiga Gasar ta Premier.

Shugaban kungiyar ya ce ''Zaha ya cancanci tafiya Manchester United domin ya samu cigaba, ina ganin yana da kyau zai shiga cikin 'yan wasansu na farko.''

Steve Parish ya ce ''mun san tafiyarsa babbar asara ce gare mu, daman wa zaka sayar fam miliyan 15 da zai zama ba asara ba?

Ya ce '' dubi Arsenal sun yi asarar Robin van Persie, babbar asara ce gare su.Wilfried Zaha shi ne Van Persien Crystal Palace.''