Aurelien Chedjou ya koma Galatasaray

Aurelien Chedjou
Image caption Aurelien Chedjou ya buga wa Lille wasannin lig 154 tun da ya koma daga FC Rouben a 2007

Dan wasan Kamaru Aurelien Chedjou ya koma kungiyar Galatasaray da keTurkiyya a kan yarjejeniyar shekaru hudu.

Dan wasan koma ne daga kungiyar Lille a kan dala miliyan takwas da dubu dari biyu.

Chedjou mai shekaru 27 zai hadu Dany Nounkeu dan uwansa dan kasar Kamaru a matsayin 'yan bayan kungiyar.

Yanzu haka dukkanninsu suna atisaye da tawagar 'yan wasan Kamarun a shirye-shiryen wasan sada zumunta da zasu yi da Ukraine ranar Lahadi.

Karin bayani