City da United na fafutukar sayen Fabregas

Cesc Fabregas
Image caption Kungiyoyin biyu sun shiga fafutukar sayen Cesc Fabregas

Manchester United da Manchester City na gogayya wajen dawo da Cesc Fabregas Gasar Premier ta Ingila a kakar wasanni ta gaba.

Sabon mai horad da 'yan wasan United David Moyes na duba yuwuwar sayen dan wasan na tsakiya bayan da Barcelona ta bayyana musu aniyarta ta sayar da tsohon kyaftin din na Arsenal.

Sai dai kuma a wata mai kama da kisisina Barcelonan ta kuma ankarar da abiyar hamayyar Man United din wato Manchester City shirinta na sayar da dan wasan.

Kuma Manchester Cityn ba tare da wani jinkiri ba ta nuna sha'awarta a kan dan wasan tsakiyar na Spaniya.

Karin bayani