Suarez na son tafiya Real Madrid

Luis Suarez
Image caption Luis Suarez ya ce, ''na gaji da abin da 'yan jaridar Ingila suke yi min''

Dan wasan gaba na Liverpool Luis Suarez ya ce abu ne mai wuya idan Real Madrid ta neme shi ya ki tafiya.

Dan wasan da ya kulla yarjejeniya ta tsawon lokaci da Liverpool wanda ya ci kwallaye 30 a bana an kuma haramta masa buga wasanni 10 saboda cizon Branislav Ivanovic na Chelsea.

Suarez mai shekaru 26 a hirarsa da wani gidan rediyon Uruguay ya kuma ce ba zai iya ci gaba da jure wahalar da yake sha daga 'yan jaridar Ingila ba.

Dan wasan wanda ya koma Liverpool daga Ajax a 2011 ya ce sukan da ya ke sha daga 'yan jaridar ya sa ya gaji.

Ya ce, '' na gaji, 'yata da matata sun wahala, ba zan iya jure wa wahalar ba haka.''

Dan wasan na Uruguay ya kara da cewa, '' na sha wahala sosai ina yaro domin zama abin da na zama yau amma kuma na zama abin muzantawa a wajen 'yan jaridar.

Ba sa yaba min a matsayin dan wasa, kawai suna maida hankali ne wajen yin hukunci a kan halayyata.''

Suarez, ya ce, ''ina jin dadi a Liverpool na gode wa magoya bayan kungiyar. Na aikata kuskure a matsayina na mutum amma kuma kafafen yada labaran sai maganganun da basu dace ba suke yi a kaina.''

Karin bayani