FIFA ta hana wariyar launin fata

Image caption FIFA ta ce matakan za su magance wariyar launin fata a harkar wasanni

Hukumar gudanarwa ta FIFA, ta amince da gagarumin rinjaye, a dauki sababbin tsauraran matakai na hukunta duk wanda aka samu da nuna wariyar launin fata da bambance-bambance a harkar wasanni.

Wakilai daga fiye da kasashe 200 mambobin hukumar sun amince da rahoton kwamatin da hukumar ta kafa karkashin jagorancin mataimakin shugaban FIFA, Jeffrey Webb, wanda ya bayyana matakan da aka dauka a matsayin wani gargadi ga masu yin wannan dabi'a a harkar kwallon kafa.

Wani taro na shekara-shekara da FIFA ta gudanar a kasar Mauritius ya amince a dauki matakan da suka hada da rage makin cancantar kungiyoyin kwallon kafa daga shiga Gasar kwallon kafar duniya, ko haramtawa kasashen da 'yan wasansu suka nuna wariyar launin fata shiga gasar kwallon kafar duniya.

A makon jiya ne dai jami'an hukumar kwallon kafa ta kasashen turai suka sanar da daukar nasu tsauraran matakan na magance wariyar launin fata a harkar kwallon kafa.

Matakan sun hada da haramtawa 'yan wasa shiga gasa sau goma da kuma rufe filayen wasa idan 'yan kallo sun keta ka'idojin wasa.

Karin bayani