Tennis: Federer ya tsallake da kyar

Roger Federer
Image caption Federer yanzu zai hadu da Jo-Wilfried Tsoga

Roger Federer ya samu damar shiga zagayen wasan gab da na kusa da karshe na Gasar French Open bayan ya sha da kyar a hannun Gilles Simon.

Federer ya fuskanci hadarin ficewa daga gasa da wuri a wata babbar gasa abin da rabon da ya gamu da shi tun 2004.

Sai dai ya yunkuro daga baya inda ya yi nasarar da ta cece shi daga wannan hadarin kunya ya kwaci kansa a turmi biyar da maki 6-1 4-6 2-6 6-2 6-3.

Da wannan nasara ta 900 a wasanninsa Federer dan kasar Switzerland mai shekaru 31 ya sami shiga wasan gab da na kusa da karshen inda zai fafata da Jo-Wilfried Tsonga.

Ita ma Serena Williams ta daya a duniya a bangaren mata ta samu nasarar zuwa wasan gab da na kusa da karshen na Gasar ta Faransa.

Ba Amurkiyar ta yi galaba akan Roberta Vinci 'yar kasar Italiya da maki 6-1 6-3 a wasan da a turmin farko ta fuskanci dan kalubale daga abiyar karawar tata.

Serena Williams wadda ke kan hanayarta ta daukar kofin na gasar ta Fransa na biyu za ta fafata ne da Svetlana Kuznetsova 'yar Rasha a gaba.

'yar Rashan ta yi galaba ne akan Angelique Kerber ta samu zuwa wannan matsayi da maki 6-4 4-6 6-3.

Karin bayani