Chamberlain ya taimakawa Ingila —Hodgson

Image caption Oxlade-Chamberlain ya taka rawar gani

Kocin Ingila Roy Hodgson ya ce dan wasan kungiyar da aka sanya daga baya a wasan da kasar ta yi da Brazil, Alex Oxlade-Chamberlain, ya taimakawa kasar suka yi kunnen-doki 2 da 2.

Brazil ce ta fara cin Ingila amma daga baya Oxlade-Chamberlain da Wayne Rooney suka zura kwallaye biyu.

Sai dai daga bisani Paulinho ya farke inda aka tashi biyu-da-biyu.

A cewar Hodgson, "Alex na cike da kuzari. Ya taimaka wajen daidaita wasan. Wasan yana tafiya daidai kafin a sanya shi. Amma ya karawa wasan armashi lokacin da ya shigo, har ma ya zura kwallo guda".

Shi ma Oxlade-Chamberlain ya shaidawa BBC cewa yana alfahari da zura kwallon da ya yi.

A cewarsa, '' Na yi kokarin inganta yadda nake zura kwallaye a Ingila, kuma na samu dama a wasan da muka yi da Ireland a makon jiya sai dai ban yi sa'a ta zura kwallo ba. Amma na shaidawa wani cewa ina fatan cin kwallo idan muka yi wasa da Brazil''.

Karin bayani