Anzhi na son kada Eto'o ya buga wa Kamaru wasa

Samuel Eto'o
Image caption Likita ya bukaci Samuel Eto'o ya huta

Kungiyar Samuel Eto'o ta Rasha Anzhi Makhachkala ta bukaci Hukumar kwallon Kamaru da kada ta sa shi a wasannin neman zuwa gasar Kofin Duniya da za su yi.

Likitan kungiyar Stijn Vandenbroucke ya ce dan wasan ya kara fama ciwon da ya ji a cinyarsa a lokacin wasan karshe na Kofin Kalubale na Rasha ranar Asabar.

Likitan klub din ya bukaci da a bar dan wasan wanda jami'an lafiya na kungiyar 'yan wasan kasar ta Kamaru za su duba ya huta tsawon makwanni.

Likitan kungiyar ta Indomitable Lions shi ne zai yanke shawara ko Eto'o zai iya wasa ko kuma ba zai iya ba.

A ranar 9 ga watan nan na Yuni Kamarun za ta kara da Togo bayan mako daya kuma ta hadu da Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo.

Kamarun ita ce ta daya a rukuni na 9,wato Group I da maki 6, inda ta dara Libya da maki daya.

Yayin da Congo ke da maki 4,Togo kuma tana da maki daya kawai.

Eto'o ya buga wasan karshen na Kofin kalubalen na Rasha da klub din nasa ya yi da CSKA Moscow na su Ahmed Musa na Najeriya tsawon mintina 120.

Klub din CSKA Moscow shi ya dauki Kofin.

Karin bayani