Ni ne zan zama sabon kocin Chelsea —Morinho

Image caption Morinho ya ce a wannan makon zai zama kocin Chelsea

Jose Mourinho ya shaidawa wani gidan talabijin na kasar Spain cewa yana sa ran a sake nada shi a matsayin kocin Chelsea a karshen makon nan.

Kocin mai shekaru 50 a duniya, ya bar Real Madrid bayan ya shafe shekaru uku yana jagoracin kulob din.

A cewarsa, '' Zan tafi London, kuma daga ranar Litinin zuwa karshen mako zan zama sabon kocin Chelsea."

Mourinho ya taba zama kocin Chelsea tsakanin shekarar 2004 zuwa 2007, kuma a lokacin ne kulob din ya lashe Gasar Premier sau biyu.

Karin bayani