Ribery ya sabunta kwantiragi

Frank Ribery
Image caption Frank Ribery ya taimakawa Bayern ta dauki kofuna uku na farko a tarihi

Frank Ribery ya sabunta kwantiraginsa da Bayern Munich da karin shekaru biyu har zuwa shekara ta 2017.

Ribery dan Faransa ya taimakawa kungiyar zama ta farko a Jamus da ta dauki kofin lig din Jamus, Bundesliga da na kalubalen kasar da kuma na Zakarun Turai a bana.

Ribery mai shekaru 30 ya bugawa klub din wasanni 43 inda ya ci kwallaye 11 a kakar wasannin da ta kare.

Dan wasan wanda ya koma kungiyar daga Marseille a 2007 ya taimaka wajen kwallaye 2 da suka ci da 1 a wasan karshe na cin Kofin Zakarun Turai da Borussia Dortmund a Wembley a watan Mayu.

Shi ma dan wasan baya dan Belgium Daniel Van Buyten ya kara kwantiragin shekara daya da kungiyar.

Bayern da ta dauki tsohon kociyan Barcelona Pep Guardiola a matsayin sabon mai horad da 'yan wasanta ta ci wasanni 15 daga 16 na karshen kakar wasannin da ta kare inda ta yi rashin nasara a daya.

Babban jami'in klub din na Bayern Munich Karl-Heinz Rummnigge ya ce, ''mun yi matukar farin ciki da muka ci gaba da rike 'yan wasan biyu.''