Brazil ta lallasa Faransa 3-0

Neymar
Image caption Neymar matashin dan wasan Brazil da ake ganin zai yi fice a gasar Kofin Duniya

Brazil ta lallasa Faransa a wasan sada zumunta na kwallon kafa da ci 3-0 a filin wasa na Arena do Grêmio da ke Brazil din.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne a minti na 54 Oscar ya fara jefa kwallo a ragar Faransa da ta bakunci Brazil din.

Minti tamanin da biyar da wasan ne kuma sai Hernanes ya biyo baya da kwallo ta biyu.

Ana shirin tashi ne kuma bayan minti 90 na wasan a karin lokacin da aka bata sai Brazil ta samu bugun fanareti wanda Lucas bai yi wata wata ba ya jefa ta a raga.

Brazil ta samu nasarar da ta bata kwarin guiwar tunkarar Gasar Zakarun Nahiyoyi da za a fara ranar 15 zuwa 30 ga watan nan na Yuni a kasar.

Brazil ita ce ta 22 a jerin kasashe gwanaye na Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa na watan nan.