Gasar Faransa: Nadal ya dauki Kofi

Rafeal Nadal
Image caption Rafeal Nadal ya shiga layin zakarun tennis na duniya

Rafeal Nadal ya jure wa matsalar mai kutse a fili da ruwan sama ya buge David Ferrer ya dauki kofin Gasar tennis ta Faransa a karo na takwas.

Nadal dan Spaniya mai shekaru 27 ya yi galaba ne a kan Ferrer shi ma dan Spaniya da maki 6-3 6-2 6-3 ya dauki kofin tare da kai kansa matsayin wadanda suka yi fice a tarihi a wasan na tennis.

Nasarar ta 59 ta sanya Nadal ya zarta Roger Federer da Guillermo Vilas a gasar ta Roland Garros.

Kofin kuma wanda shi ne na 12 na wata babbar gasa da ya dauka ya sa ya wuce Bjorn Borg da Rod Laver a tarihi.

Ferrer wanda wannan shi ne karon farko da ya zo wasan karshe na wata babbar gasa yana shekara 31 ya yi kokari fiye da yadda aka yi tsammani sai dai bai zamar wa zakaran wata barazana ta sosai ba.

Wasan karshen ya gamu da 'yar matsalar zanga zanga a cikin 'yan kallo sannan kuma wani dan kallo ba riga a jikinsa kuma ya sanya abin kare fuskarsa na badda kama ya kutso cikin fili da wuta a hannu amma jami'an tsaro suka kama shi.