Kocin Najeriya ya sauya 'yan wasa

Stephen Keshi
Image caption Stephen Keshi ya surka tawagar 'yan wasan Najeriya da sababbi

Najeriya ta yi gagarumin sauyi a tawagar 'yan wasanta na Super Eagles inda ta maye gurbin tara daga cikin wadanda suka ciyo mata Kofin Afrika a watan Fabrairu.

Daga cikin sauye-sauyen mai horad da 'yan wasan kasar Stephen Keshi ya kawo wasu sabbin 'yan wasa hudu da ba su taba buga wa kasar wasa ba da zai je Gasar Zakarun Nahiyoyi a Brazil da su.

Victor Moses da Emmanuel Emenike ba sa cikin tawagar haka kuma bai sanya Peter Odemwingie da Obafemi Martins ba.

Najeriya tana rukuni na biyu wato Group B da ya kunshi Tahiti da Uruguay da Spaniya.

Brazil da Japan da Mexico da Italiya kuma suna rukuni na farko wato Group A na Gasar ta Zakarun Nahiyoyi.

A ranar Laraba Najeriya za ta je Namibia inda za su kara a wasan neman zuwa gasar Kofin Duniya kafin tawagar ta nufi Brazil.

Najeriya ita ce ta daya a rukuninta da tazarar maki biyu a kan Malawi yayin da ya rage wasanni biyu a kammala.

Ga tawagar 'yan wasan Najeriyar:

Masu tsaron gida: Chigozie Agbim (Enugu Rangers), Austin Ejide (Hapoel Beer Sheva), Vincent Enyeama (Maccabi Tel Aviv)

'yan baya: Efe Ambrose (Celtic), Francis Benjamin (Heartland FC), Elderson Echiejile (Sporting Braga), Azubuike Egwuekwe (Warri Wolves), Solomon Kwambe, Godfrey Oboabona (both Sunshine Stars), Kenneth Omeruo (ADO Den Haag)

'yan wasan tsakiya: Emeka Eze (Enugu Rangers), John Obi Mikel (Chelsea), Fegor Ogude (Valerenga), John Ogu (Academica Coimbra), Ogenyi Onazi (Lazio), Sunday Mba (Enugu Rangers)

'yan gaba: Joseph Akpala (Werder Bremen), Michael Babatunde (FC Kryvbas), Muhammad Gambo (Kano Pillars), Brown Ideye (Dynamo Kiev), Ahmed Musa (CSKA Moscow), Nnamdi Oduamadi (Varese), Anthony Ujah (FC Cologne).