Zanga zangar auren jinsi a Gasar Faransa

jami'in tsaro ya rike mai zanga zanga rike da wuta a Gasar Faransa
Bayanan hoto,

Jami'in tsaro ya rike mai adawa da auren jinsi a Gasar Faransa rike da wuta

Masu adawa da auren jinsi sun yi yunkurin kawo tarnaki a lokacin wasan karshe na Gasar Faransa ta maza.

Wani dan kallo da ya rufe fuskarsa da abun badda kama kuma babu riga a jikinsa kuma yana rike da 'yar sanda da ke cin wuta ya kutso cikin fili amma aka damke shi kafin ya shiga filin.

Kimanin minti biyu kafin wannan ma wasu mutanen biyu a cikin 'yan kallo ba riga sun bayyana dauke da kyalle mai rubutu da ke sukar lamirin kasar Faransa da take hakkin yara.

Sauran masu zanga zangar kuma sun yi kira ne ga Shugaba Francois Hollande ya sauka daga mulki.

Matakin da Faransa ta dauaka na halatta auren jinsi daya shi ya harzuka masu zanga zangar.

A watan da ya wuce ne aka daura auren farko na 'yan luwadi a Faransan karkashin tsauraran matakan tsaro.

Jami'an tsaro sun gaggauta kawo karshen zanga zangar a lokacin wasan na karshe na Roland Garros wanda Rafeal Nadal ya dauki kofin.