Andre da Jordan Ayew sun komawa Black Stars

Image caption Andres da Jordan Ayew

Andre da Jordan Ayew sun amince su koma bugawa Ghana kwallon kafa bayan tattaunawar da suka yi da shugaban kasar, John Mahama.

A watan Fabarairu ne 'yan gida dayan, suka ce sun daina bugawa Black Stars kwallo saboda rashin jituwa da mahukunta kwallon kafa a kasar.

Rahotanni sun nuna cewar 'yan wasan na Olympique Marseille sun gana da Shugaban Ghana a ziyararsa daya kai a Faransa.

Bayan tattaunawar ce kuma suka amince su dinga bugawa Black Stars kwallo.

Andre ya ce "Komai a yanzu ya yi dai, ina saran hukumar kwallon Ghana zata gyaru".

Ministan wasanni Ghana, Elvis Afriyie Ankrah ya ce Shugaban kasar ya shiga tsakanin ne saboda ganin cewar kasar ta ci ribar yawan 'yan wasan da take dasu.

Karin bayani