Ana zargin Messi da kin biyan haraji

Image caption Gwarzon dan kwallon duniya, Lionel Messi

Ana binciken dan kwallon Barcelona Lionel Messi da mahaifinsa a kasar Spaniya bisa zargin kin biyan harajin kusan Euro miliyon hudu.

Hukumomi a Spain, sun ce dan kwallon Argenina da mahaifinsa, Jorge, ana zarginsu da mika takardun bogi a kan harajin da suka biya a shekarun 2007 zuwa 2009.

Messi dan shekaru ashirin da biyar da haihuwa kuma gwarzon dan kwallon duniya, kawo yanzu bai maida martani ba a kan zargin.

Albashinsa a Barcelona ya kai kusan Euro miliyon goma shida a duk shekara.

A ranar Laraba, mai shigar da kara, Raquel Amado ya gabatarwa kotu takara a lardin Barcelona inda a nan Messi ke zaune.

Dole sai alkalai sun amince da koken, kafin a tuhumi wadanda ake zargin.

Karin bayani