Ingila bata san yadda za ta buga wasa ba–Redknapp

Image caption Redknapp ya soki yadda Ingila ke buga wasa

Mai bada horo na Kungiyar Kwallon kafa ta Queens Park Ragers, Harry Redknapp ya yi amannar cewa Ingila bata san yadda za ta buga kwallon kafa ba sannan kuma ya nuna goyon bayan sa ga Glenn Hoddle ya jagoranci tawagar 'yan wasan kasa da shekaru 21.

Tawagar 'yan kasa da shekaru ashirin da daya na Ingila sun gaza cimma wani matsayi a gasar cin kofin zakaru na Nahiyar a wannan shekarar; a karkashin jagorancin Stuart Pearce.

Redknapp, an sa ran zai gaji Fabio Capello a matsayin mai bada horo na tawagar manyan 'yan wasan kasar a 2012 amma aka nada Roy Hodgson.

Redknapp, wanda ya samu nasarar cin kofin FA da Portsmouth a shekarar 2008, ya jagoranci Tottenham zuwa fitowar gasar cin kofin zakaru a 2010 kafin a danganta shi sosai da zama kociyan Ingila a 2012.

Karin bayani