Brazil: Zanga-zanga a wajen gasar nahiyoyi

Image caption Masu zanga-zangar sun ce ya kamata a inganta asibitoci da ilimi

Zanga-zangar da wadansu 'yan kasar Brazil suka yi a lokacin bude gasar nahiyoyin duniya ta yi sanadiyar raunatar mutane 39.

Kimanin 'yan kasar 1000 ne suka yi zanga-zanga a kusa da babban filin wasa na kasar don nuna kin amincewarsu da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na ware makudan kudi don daukar nauyin gasar cin kofin duniya.

'Yan sanda sun fesawa masu zanga-zangar barkonon-tsohuwa don tarwatsa su gabanin fara wasan, wanda Brazil ta casa Japan da ci uku ba ko daya.

Wadansu rahotanni sun ce 'yan sandan sun yi amfani da harsasai na roba wajen tarwatsa masu zanga-zangar, kuma sun kama kimanin mutane 30.

Masu zanga-zangar sun rike takardun da aka rubuta, '' ba ma so a gudanar da gasar cin kofin duniya. Muna so a yi amfani da kudinmu don inganta asibitoci da ilimi.''

Karin bayani