Liverpool na zawarcin Henrikh

mai horar da 'yan wasan liverpool brendan rodgers
Image caption manajan kulob din liverpool

Liverpool na yunkurin sayan dan wasan tsakiya dan kasar Armenia Henrikh Mkhitaryan.

Dan wasan dai zai zamo babban dan wasan da za su saya, kafin kakar wasanni mai zuwa.

An gano cewa karkashin kwantiragin da dan wasan mai shekaru 24 ya sanyawa hannu a kulob din Shaktar Donetsk, za a biya pam miliyan ashirin idan za a siyar da shi ga wani kulob din.

Kulob din Liverpool ta ce a shirye ta ke ta biya kudin.

Jami'an Liverpool sun san cewa za su fuskanci gasa a sayen Mkhirtayan, wanda ya ci wa kulob din Shekhtar kwallo 25 a kakar wasannin bara, amma duk da haka ake son ya koma Liverpool.

Manaja Brendan Rodgers yana son sayen Mkhitaryan wanda su ma kulub din Juventus, da Borussia Dortmund ke neman sayensa, a matsayin dan wasan da zai kara kuzari a kulob dinsa a kakar wasanni ta gaba.

Harwayau Liverpool na tattaunawa da Sunderland dan sayan mai tsaron ragarta Simon Mignolet.

Sun yi tayin pam miliyan 8, amma Sunderland ta dage akan pam miliyan 10, amma ana saran za su daidaita.

Manaja Rodgers ya kuma sayi dan wasan baya na kulob din Manchester City Kolo Toure.