FA ba za ta sabunta kwantiragin Pearce ba

Image caption FA ta ce ba za ta sabunta kwantigarin Stuart Pearce ba

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ce ba za ta sabunta kwantiragin kocin kungiyar kwallon kafa 'yan kasa da shekaru ashirin da daya, Stuart Pearce, idan kwantiraginsa ya kare a karshen watan nan.

Pearce, mai shekaru 51 a duniya, ya jagoranci kungiyar kwallon kafar tsawon shekaru shida.

An soki Pearce, wanda tsohon kocin Manchester City ne da 'yan wasansa bayan an fitar da Ingila a farko-farkon gasar cin kofin zakarun Turai na 'yan kasa da shekaru 21 a watan da muke ciki.

A cewar shugaban FA, David Bernstein, '' Ina son godewa Stuart Pearce saboda aikin da ya yi tukuru. Babu wanda yake shakka game da aikin da ya yi a matsayin kocin 'yan kasa da shekaru 21''.

Bernstein ya kara da cewa kodayake Pearce ya yi aiki sosai don ganin kungiyar ta shiga zagayen karshe na gasar, yana mai cewa matsalolin da ya samu a baya ne suka sanya za a sauya shi.

Karin bayani