Za a kammala Premier kafin FA

Image caption Za a kammala wasannin Premier kafin wasan karshe na FA

Wasan karshe na gasar cin kofin FA za a yi shi bayan an kammala wasannin kakar bana na cikin gida abinda ba a yi hakam ba tun shekara ta 2010.

Wasannin gasar cin kofin Premier na Ingila guda hudu an yi su ne rana guda a wasan karshe na shekara ta 2011, inda Machester United ta yi nasara a kan Blackburn.

Amma a shekara ta 2014 wasan karshen za a yi shi ranar 17 ga watan Mayu; a karshen mako bayan wasannin zagaye na gasar Premier.

A shekara ta 2011, Manchester City ta sami nasara kan Stoke a wasan karshe na FA kuma a rana daya da Manchester United ta ci gasar Premier.

Karin bayani