An fitar da wasannin gasar premier

'Yan wasan kulob din Manchester United
Image caption 'Yan wasan kulob din Manchester United

An fitar da jerin wasannin da za a buga a gasar wasannin premier na 2013 zuwa 2014, inda manajan kulob din Manchester United, David Moyes ya samu dama ta farko na buga wasa a Swansea.

Shi kuwa Jose Mourinho wanda zai jagoranci kulob din Chelsea a karo na biyu, zai dauki bakuncin kulob din Hull a ranar 17 ga watan Agusta.

Manuel Pellegrini zai jagoranci wasa na farko a kulob din Manchester City, inda za su kara da kulob din Newcastle a filin wasa na Etihad.

Kulob din Cardiff kuwa zai yi tattaki ne zuwa West Ham, yayin da Crystal Palace zai dauki bakuncin Tottenham.

Ita kuwa QPR wacce tauraruwarta ta rage haske, za ta fara wasa a gasar zakarun nahiyar Turai, inda za ta dauki bakuncin Sheffield a ranar Laraba 3 ga watan Augusta.

A sabon kakar wasannin Arsenel za ta fafata a gida ne da Aston Villa, yayin da Sunderland kuma za ta dauki bakuncin Fulham, ita kuwa Southampton za ta yi tattaki zuwa West Brom.

Bayan wasan da suka yi a Swansea, United za ta dauki bakuncin Chelsea a filin wasa na Old Trafford.

Daga nan ne kuma Man U za ta kece raini da Liverpool a karshen makon dake tafe.

A karon batta na farko a kakar wasannin na bana kuwa, Manchester City za ta kece raini da Manchester United a ranar 21 ga watan Satumba.

Inda kuma za su sake garzaya wa zuwa Old Trafford su maimaita karon battar a ranar 22 ga watan Maris na badi.