Emenike zai iya buga wasa da Malawi

Image caption Emenike zai iya buga wasan Malawi

Fitaccen dan gaban Najeriya nan Emmanuel Emenike na shirin dawowa Tawagar Super Eagles don ya buga wasan da yake da mahimmanci na neman fitowa gasar cin kofin duniya da kasar Malawi a watan Satumba.

Emenike, ya murmure ne daga rauni da ya samu a gwiwa kusan watanni shida da suka wuce.

Gogaggen dan wasan ya ce "bayan watanni biyar, Ina fatan bugawa kasa ta wasa a watan Satumba."

Najeriya dai za ta samu nasarar fitowa gasar cin kofin kwallon kafa na duniya shekara ta 2014 matsawar Malawi bata yi nasara akanta ba a gida.

Ita ma dai Malawin na da bukatar cin Najeriya a wasan kafin ta fito gasar.

Karin bayani