Ingila za ta dawo da dabarun kwallonta—Taylor

Image caption 'Yan wasan Ingila na buga wasan gasar yan kasa da shekaru 20

Mai horos da 'yan Kungiyar kwallon kafa ta Ingila na 'yan kasa da shekaru 20, Peter Taylor, ya ce tawagarsa za ta dawo da martabar kwallon kafar kasar a gasar 'cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 20.

Tawagar dai ta Ingila a gasar zakarun Turai na 'yan kasa da shekaru 21 ta ba da kunya, inda aka yi waje da su bayan cin su wasanni uku da aka yi a matakin rukuni-rukuni.

Taylor dai na cewa sun yi kokari amma dai wasan ya ba su kunya.

A ranar Lahadi ne tawagar za ta fara wasanta a Turkiyya inda za ta kara da Iraqi.

Karin bayani