Lago Aspas zai koma Liverpool

Image caption Liverpool ta sayi Lago Aspas

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta sayi dan wasan gaba na Kungiyar kwallon kafa ta Celta Vigo, Lago Aspas, a kan kudi Fam miliyan bakwai.

Kulob din ya amince da cinikin a makon da ya gabata suna kuma jira a kammala duk wani rubuce-rubuce kafin su tabbatar da kwantaragin mai tsawo.

Dan wasan dan kasar Spaniya mai shekaru 25 ya zura kwallaye goma sha biyu a wasannin talatin da biyar ga Kulob din Celta wannan kakar.

Dan wasan dai ya zama shine na biyu dan kasar Spaniya da kulob din ya sa hannu a kansa a karshen mako, bayan da suka sayi dan wasan Sevilla da kuma dan wasan Spaniya na 'yan kasa da shekaru 20, Luis Alberto.

Karin bayani