Guardiola na samun matsin lamba

Image caption Guardiola na fuskantar matsin lamba

Pep Guardiola ya yi amannar cewa ana matsa masa lamba a kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich don ya kwaikwayi irin nasarorin da wanda ya gada, Jupp Heynckes, ya samu.

Dan kasar Spaniyar mai shekaru 42 ya fadi maganar ne a wani taron manema labarai na farko da ya yi a matsayinsa na sabon mai ba da horo na kulob din.

Kulob din Bayern a karkashin jagorancin Heynckes, tsohon mai ba da horon, ya zama kulob din Jamus na farko da ya samu nasarar lashe gasar Bundesliga da Kofin Turai da kuma na Jamus a kakar wasanni daya.

Amma duk da nasararorin da tsohon kocin ya samu, Kulob din ya sanar da shi cewa ba za su kara kwantaraginsa ba saboda Guardiola.

Karin bayani