Hull City ta sayi Curtis Davies

Image caption Hull City ta sayi Curtis Davies

Kungiyar kwallon kafa ta Hull City ta rattaba hannu a kwantaragi da tsohon dan bayan Aston Villar nan Curtis Davies daga Birmingham.

Dan wasan dai bai bayyana kudaden da aka saye shi ba amma ana ganin kamar zai kai fam miliyan biyu da dubu dari biyu da hamsin.

Davies ya fara wasa ne a birnin Luton kafin ya matsa zuwa West Bromwich.

A shekara ta 2007 dan wasan ya tafi Aston Villa aro kafin a saye shi a kulob din kan kudi Fam miliyan tara da dubu dari biyar kafin ya rattaba hannu a kwantaragin Birmingham a shekara ta 2011.

Karin bayani