Najeriya na tunkarar gasar zakarun Afrika

Image caption Najeriya na tunkarar gasar Zakarun Afrika

Najeriya na fatan su ci wasan su na gida wanda zai ba su damar bayyanar su a gasar cin kofin zakaru na Afrika.

Super Eagles za su tunkari Ivory Coast sau biyu inda wasan na farko za ayi a Kaduna shida ga watan Yuli, wanda ya samu nasara kuma zai je Afrika ta kudu don gasar.

Zakarar Afrikar dai wato Najeriya na son murmurewa daga rashin nasarar da suka yi a gasar cin kofin Nahiyoyi, inda suka kare a na uku a wasannin rukuni-rukuni.

Kociyan Super Eagles Stephen Keshi, ya shaidawa BBC cewa gasar cin kofin Nahiyoyi ya zama darasi ga 'yan wasan su na gida, amma su na da damar da za su nuna abin da suka sami darasin a gasar Zakarun.

Karin bayani