Brazil ta tsallake zuwa zagayen karshe

'Yan wasan Brazil na murna bayan cin kwallonsu na hudu
Image caption 'Yan wasan Brazil na murna bayan cin kwallonsu na hudu a gasar

Kungiyar kwallon kafa ta kasar Brazil ta tsallake zuwa zagayen karshe a gasar cin kofin nahiyoyi, inda za ta kara da Spaniya ko Italiya.

Brazil ta samu nasarar ne, bayan doke Uruguay da ci 2-1.

A ranar Lahadi mai zuwa ne za a yi karawar zagayen karshen, a filin wasa na Maracana na Rio de Janeiro.

Fred ne ya fara ciwo wa Brazil kwallonta na farko a kashi farko na wasan, kafin Edinson Cavani ya farke wa Uruguay bayan hutun rabin lokaci.

Amma daga bisani Brazil ta jefa kwallo na biyu da ya bata nasara a taka ledar.