Tevez na alfaharin sa riga mai lamba 10

Image caption Tevez na alfaharin sa rigar bal lamba 10

Sabon dan wasan gaban Juventus Carlos Tevez ya ce ya na alfahari da sanya rigar kulob din mai lamba 10 bayan da aka kammala sayensa daga Manchester City a kan kudi fam miliyan 12.

Dan kasar Argentina, mai shekaru 29, shi ne dan wasa na baya bayan nan da ya sa rigar 'yan bal da a baya su Alessandro Del Piero da Michel Platini da kuma Roberto Baggio suka saka.

Tun lokacin da tsohon Kyaftin din Juventus Del Piero ya koma Sydney a kakar wasannin bara babu wanda ya sake amfani da lambar.

Amma Tevez ya nuna farin cikinsa da saka lambar inda yake kwatanta ta da lambar da tsohon gogaggen dan wasan Argentina Maradona ke sawa.

Karin bayani