Cisse zai bar Queens Park Rangers

Djibril Cisse zai koma Qatar a matsayin aro
Image caption Djibril Cisse zai koma Qatar a matsayin aro

Djibril Cisse zai koma kungiyar Al-gharafa ta Qatar a matsayin aro daga ranar 1 ga watan Yuli.

Hakan ta samu ne bayan wata rijejeniya ce da bangarorin biyu suka amince da ita.

Mai shekaru 31, Cisse ya ci kwallaye hudu a wasanni 21 a kakar wasa da ta gabata.

A shekara ta 2012 ya buga wasa 29 tare da saka kwallaye 10.