An yi waje da Ingila a U-20

Image caption An yi waje da Ingila gasar U- 20

An yi waje da Ingila a gasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 20 bayan da Masar ta lallasa ta da ci biyu ba ko daya.

'Yan wasan da Peter Taylor ya jagoranta na bukatar cin wasan don kaiwa wasannin zagaye na biyu a Turkiyya amma aka doke su.

Ingilar dai ta yi canjaras ne a wasannin ta biyu na rukuni-rukuni; ta yi biyu da biyu da Iraqi sannan kuma ta yi kunnen doki da Chile.

Fitar da Ingilan akayi na zuwa ne bayan da 'yan wasan su na gasar cin Kofin Turai na 'yan kasa da shekaru 21 su ma aka yi waje da su inda ba su ci wasa ko daya ba a wasannin rukuni-rukuni guda uku.

Karin bayani