An yi waje da Masar a gasar U-20

Image caption An yi waje da Masar a gasar U 20

Kasar Masar an yi waje da ita a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na 'yan kasa da shekaru 20 duk kuwa da lallasa Ingila da ta yi da ci biyu ba ko daya a wasan su na karshe na rukuni-rukuni.

Masar dai ta samu nasarar ne inda Mahmoud Trezeguet da kuma Hassan Ahmed suka ci kwallaye biyu.

Kasashen Ghana da Najeriya ne dai a Afrika suka fito zagaye na biyu; Mali da Masar kuwa an yi waje da su.

Duk da mamaye wasan da Ingila ta yi a wasanta da Masar amma ta kasa zura kwallo a ragar Masar din inda mai tsaron gida Awad Mossad ya yi ta kade kwalleyen da suka kusan ci.

Karin bayani