A Najeriya Hukumar Kwallon Kafa ta soki Keshi

Image caption Stephen Keshi ba zai sake zabar 'yan wasa ba shi kadai

Shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya, Aminu Maigari, ya bayyana cewa mai bada horo Stephen Keshi ba zai sake kasancewa mai zaben 'yan wasa ba shi kadai.

Maigari, ya soki zaben 'yan wasan da Keshi ya yi a gasar cin kofin Nahiyoyi wanda aka yi waje da Najeriya a matakin rukuni-rukuni, ya kuma ce bai gamsu da tsarin tawagar ba a yanzu.

Acewar Shugaba Maigari, " gasar cin kofin Nahiyoyi babbar gasa ce shi yasa shauran kasashen suka fito da gogaggun 'yan wasansu."

Ya ce kasar Spaniya ta fito da gogaggun 'yan wasanta, amma Najeriya ba ta yi haka ba.

Karin bayani