Brazil ta yi rawar gani a Maracana

Image caption Brazil ta yi rawar gani a Maracana

Kasar Brazil ta yi rawar gani a filin wasa na Maracana inda ta bawa Spaniya mamaki da ci uku ba ko daya abin da ya bata nasarar cin kofin Nahiyoyi karo na uku a jere.

'yan kallo dai sun cika makil a wasan da aka yi a daren jiya lahadi inda zakarun kwallon kafa na duniya sau biyar suka nuna aniyar su ta nuna kwarewa bisa irin wasan da suka yi a wasan karshen.

Bayan Alkalin wasa ya busa usur na tashi daga wasan, masoya kwallon kafa na Brazil na ta rera wakoki suna cewa "Zakaru sun dawo".

Brazil dai ta jima a fagen wasan kwallon kafa ta na nuna bajin ta da kwarewa wajan buga kwallon abin da ya sa ake musu lakabi da Samba.

Karin bayani