Cardiff ta sayi Andreas Cornelius

Image caption Cardiff ta sayi Andreas Cornelius

Kungiyar kwallon kafa ta Cardiff City ta sayi dan wasan nan na da yake bugawa Kasarsa Denmark wasa Andreas Cornelius daga Kulob din FC Copenhagen a kan kudi Fam miliyan bakwai da rabi.

Dan wasan dan gaba an duba lafiyarsa a ranar Litinin kuma ya rattaba hannu a kan kwantaragi na shekaru biyar da Kulob din sabin shiga a Premier League.

Dan wasan mai shekaru ashirin, shine yafi kowane dan wasa cin kwallo a shekara ta 2012-2013 a gasar SuperLiga na Denmark inda ya zura kwallaye 18 a wasanni 32.

Ana martaba Dan wasan a Denmark inda ya bayyana a wasannin kasarsa na 'yan kasa da shekaru 18 da 19 da kuma 20 kafin ya buga wasan kasa da kasa da Czech Republic a watan Satumba 2012.

Karin bayani